Haber Giriş:
Turkish Airlines ya dakatar da zuwa Isra'ila

Ba a bayyana musabbabin dakatarwar ba.
Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya sanar da dakatar da zuwa Isra'ila daga ranar 26 ga Janairu zuwa 31 ga watan.
Kamfanin ya bukaci fasinjojin da za su je kasar a wannan lokaci da su tuntube su tare da sauya tikitinsu ko sanin balin da ake ciki ta kan lambar wayarsu kamar haka: 850330849 ko su tuntubi ofishin da suka sayi tikitin.