Haber Giriş:
Kasa ta zaftare tare da yin ajalin mutane da dama a Indonesiya
Mamakon ruwan sama ya janyo zaftarewar kasa a Indonesiya.
Mutane 13 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon afkuwar zaftarewar kasa da mamakon ruwan sama ya janyo a Tsibirin Jaba na Imdonesiya.
Zaftarewar kasar ta afku a kauyen Jihanjuang na yammacin Tsibirin.
Ana ci gaba da gudanar da aiyukan bincike don kubutar da mutane.
Haka zalika ana sa ran za a ci gaba da samun mamakon ruwan sama a yankin.